Addini

[Addini] FARILLAN ALWALA DA SAURANSU

FARILLAN ALWALA
Farillan alwala guda 7 neh:
•niyya
•wanke fuska
•wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
•shafar kai
•wanke kafafuwa
•cuccudawa
•gaggautawa
SUNNONIN ALWALA
•wanke hannaye zuwa wuyan hannu
•kuskure baki
•Shaka ruwa
•fyacewa
•juyo da shafar kai
•shafar kunnuwa
•sabunta ruwa agaresu
•jeranta tsakanin farillah
MUSTAHABBAN ALWALA
•yin bismillah
•goga asuwaki
•Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
•farawa daga goshi
•jeranta sunnoni
•qaranta ruwa a nisa gabobi
•gabatar da dama kafin hau.
AKAN FASALIN ALWALA
•wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun.
•idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba.
•wanda kuma ya mance lam’a sai ya wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah by an faruwar hakan toh sai ya sake ta
•wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to bazai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai yayi su
•tsettsefe ‘yan yatsu hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe ‘yan yatsun qafafuwa, tsefe gemu mara dubu yana wajaba acikin alwala, tsefe gemu yana wajaba acikin wanka koh da mai duhu neh.
AKAN FASALIN ALWALA (2)
•babu yana halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur’ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan juzu’i neh ga mai neman ilimi acikinsa.
•yaro a wajen taba al qur’ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya bashi al qur’anin ya taba.
•wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah ya ki ya she mu.
ABUBUWA MASU WARWARE ALWALA
karrai da sababai
*karrai*sune:
•fitsari
•bayan gida
•war rihu (tusa)
•maziyy
•wadiyy
*sababai*sune:
•bacci mai nauyi
•suma
•farfadiya
•marisa
•maye
•hauka
•sumbanta
•shafar mace, idan anyi da niyyar jindadi ko kuma ya samu jindadin babu nufi.

Haiman Khan Raees @HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.