AKWAI WANI KUSKURE DA MUKE YI
A
SALLAH, TO DUK WANDA YAKE YI
BASHI DA
SALLAH. (Sai mu karanta domin
mu gyara).
Wato ‘yan uwana akwai wani
kuskure da
muke yawan aiwatarwa yayin
ganawa da
Ubangijinmu shi ne kamar haka:
Zaku ga mutum idan anyi ruku’u
saboda yana
gaggawar samun wannan
raka’ar, ba ya
tsayawa yayi kabbarar harama, sai
kawai ya
zarce shi ma da ruku’un. Mun
manta da cewa
duk wanda ya manta bai yi
kabbarar harama
ba bashi da Sallah. Ka fara yin
harama tukunna sai kayi kabbarar
wannan
ruku’u da kazo ka tarar.
Kuma nasha ganin manya
da yara suna yin wannan dabi’a,
don haka
Manzo (S.A.W) ya umarce mu da
cewa kada
mu yi gudu ko gaggawa a yayin
da aka tayar
da Sallah, mu tafi a cikin nutsuwa
muje mu
sallaci raka’ar da muka samu, mu
kawo
wadanda suka wuce mu.
Domin koda zaman tahiyar karshe
ka samu to
kana da ladan jam’i amma
katashika kawo
raka’o’in da suka wuceka.
Dan Allah ‘yan uwa duk wanda
yaga wannan
sako ya aikawa yan uwa Musulmi
ta hanyar
share da Comment don mu samu
ladan
tunatarwa baki daya.
Allah ya kara fahimtar damu
addininsa.
Ameen
mudanyi shere dinsa a wasu page din dan wasu
ma su karau da abin
Souce in Bakandamiya
Wanda ya rubuta
Lawi yusuf mai gidan sama
Add Comment