Adam Zango Baifi Kowane Bahaushe Suna A Duniya Ba -Follocome


0 244

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ADAM A ZANGO BAIFI KOWANNE BAHAUSHE SUNA A DUNIYA BA

Daga Abdulhadi Followcome

Yan Kwanaki da suka gabata naji jarumi Adam a zango yana Sanarwa duniya cewar shine bahaushen da yai fice a duniya.

Wannan magana bagaskiya bane a tunina Adam a zango ya fadi hakanne kawai don farfado da tauraruwarsa data fara disashewa a harkar film dama Duniya baki daya.

Kasancewar masana’antar film din Hausa ta Dan rage yayinsa dakuma saka shi a finafinan Hausa.

Sannan harkar film dinma tafara jadabaya bakamar yadda take Adaba hakan yasaka dayawa daga cikin jaruman Hausa yiwa Kansu film dakansu dakuma kudinsu.

Hakannne yasaka jarumai da dama tsunduma cikin harkar siyasa da wakoki da editing da dai sauransu.

Adam a zango na daya daga cikin Wanda ya rungumi harkar waka da shiga cikin harkar siyasa da dai sauransu.

Kuma Adam a zango yana amfani da wallafa Abubuwan da zasu jawo CeCe kuce a internet don farfado da sunansa akansa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 341

- Advertisement -

Misali. Adam a zango yataba wallafa cewar bashida digree amma yafi kowanne mai digree samun rifin asiri.

Hakan bakaramin cece kuce yajawoba a social media ba akaita yayata sunansa.

Antaba hira da Adam a zango a gidan TV nanma yadauki alkurani yadora akansa har yai rantsuwa. Wannanma yajawo CeCe kuce a social media.

Batun cewa yafi kowane bahaushe suna a duniya wannan bakomai bane face nemarwa kai suna.

Ko Muhammad Buhari. kwankwaso. Ahmed Musa. sheikh dahiru Usman bauchi. Sheikh Bala Balau. Sheikh Kabiru Gombe. Sheikh Zazzaky Duk sunfi Adam a zango suna a duniya.

Misali. Babu kasar da muhammadu Buhari zai Shiga a duniya da ba’asansaba. Kana cewa Nigeria a duk duniya to Muhammad Buhari za a saka

Maganar cewa Adam a zango yana Tara dubbannan mutane a cinema.

Idan aka kwatanta mutanen da suke halartar kallan film din Adam a zango a sinima da Wanda sheikh dahiru usaman bauchi Yake Tarawa a mauldinsa ai bama sai ance kahadaba. Babuma hadi.

Idan muka koma India saudia China America England babu inda ba’asan Ahmed musaba. Kaga bazaka taba hadashi da Adam a zango a duniya ba

Don haka ni a ra’ayina Adam a zango yana Neman sunane kawai. Koshi kansa yasan baifi kowa suna a duniya ba

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.