Adam A Zango Ya Zama Gwarzon Jaruman Kannywood Na Shekarar 2020

0 1,726

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sanannen Jarumin nan a masanaantar Kannywood Adam A Zango ya lashe gasar zama fitaccen Jarumi na shekarar 2020.

Jaridar Online ta Amintacciya ce takeshirya gasar inda ko a kwanakin baya mabiyan ta suka zabi Hamisu Breaker matsayin Gwarzon Mawaki a wannan karon kuma Jaridar ta nemo yan Film suma guda 10 a cikin su Adam A Zango shi yai nasarar zama zakara.

Yadda jaridar ke gudanar da zaben shine jaridar ta fitar da cewa zatai zaben ne ta hanyar sanya hotunan wadanda ake gasar dasu, duk wanda yafi samu wadanda sukai like da hoton sa shi zaiyi nasara.

A cikin yan film din, da jaridar ta wallafa hotunan su Adam A Zango shine wanda yafi samun wadanda sukai like da hoton nashi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 344

Jaridar ta Amintacciya ta fitar dashi a matsayin Gwarzon Jarumin ta a 2020 inda ta bayyana cewa ba ita tai zaben ba mabiyanta ne.

A karshe wannan Jarida tana taya fitaccen Jarumi Adam A Zango Murnar samun wannan Nasara daga Mabiyan ta.

Kuma shugabannin jaridar sunyi alkawarin bashi takardar shaidar wannan gasa anan gaba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: