Adalcin INEC Ko Akasin Haka Shi Ne Makomar Jihar Kano, inji Bashi Tofa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Hadakar ma su kishin Kano karkashin shugabancin Dattijo kuma daya daga cikin Dattawan Kano Tsohon dan takarar shugaban kasa a rushashshiyar jam’iyyar NRC a Jamhoriyya ta uku Alhaji Bashir Othman Tofa Shugaban ‘Kano Concerned Citizens Initiatibe’ ya bayyana cewa nauyi gaba daya ya haukan hukumar zabe mai zaman kanta ne a Kano a yayin da za’a gudanar da sake sabe a wasu akwatuna sama da 170 a Kano a cikin wasu kananan hukumomi na Kano to adalci da hukumar zabe ta yi ko akashin haka su za’a dorawa duk wani abu da ya biyobaya ga al’ummar Kano dan haka kiransu da Hukumar zabe da ta tabbatar ta yi abunta tsakanin ta da Allah ba dun biyan bukatar wani mutum ko wata jam’iyya ba domin kuwa ita ce take da alhakin kumai kuma kashe bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.

Dattijo Alhaji Bashir Othman Tofa ya bayyana haka ne a lokacin wani gagarumin taro da ya yi da yan Jarida na gida da kafofin yada labaran wajen Nijeriya a cibiyar yan Jarida da ke birnin Kano a wannan Litinin inda wakilinmu ya samu halartar taron manema labaran da aka gabatar a NUJ Birnin Kano.

Talla

Haka kuma jigo na gaba da suke da rawar takawa na tabbabatar da tsaro da zaman lafiyar Kano ita ce Rundunar yan sandan Kano da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro don haka akwai bukatar su tsaya tsayin daka ba tari da sun zuciya ko biyan bukatar wani ba domin dai koma maye zaman lafiya shi ake so shi Kano ta yi suna akai kuma shi ta gada shi koma ake so aga ya ciga ba a birnin Kano dan haka baza muyar da wani yazo ya kawo mana cikas ku ya dagulamana zaman lafiyar kano ba inda kuma ya bukaci rundunar yan sanda da tatabbatar da hana bakin haure daga waje Kano shigowa Kano a lokacin zaben ranar 23/3/2019 ba domin tabbatar da zaman lafiya, inda kuma ya bukaci al’ummar Kano da su zama masu bin doka da oda domin bai wa hukumomin tsaro hadin kai akoda yaushe.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Haka zalika suma yan Jarida su tabbatar sun yi aikinsu kamar yadda doka ta tana da kuma su yi taka tsan-tsan kuma su cire sun zuciya ku ra’ayin siyasa ku bangaranci a cikin aikinsu na Jarida wanda mutane suke karantawa suke sauraro dama suke gani kuma ake yarda da maganar su da ganin girmansu a matsayin mutane masu kawo ci gaba don haka su sanya tsoron Allah da adalci da sanin ya kamata a cikin aikin su kamar yadda dokar aikin Jarida ta tsara musu kuma suka samu huru akan aikin Jarida.

Danga ne da matasa kuwa Tofa ya ce su sani su su ne manyan gobe kada su yarda yan siyasa su bata musu ryuwa ta hanyar tunzirasu da yin bangar siyasa domi tada hatsaniya ko rikici da haka su sani su ne makomar Jihar da Kasa take hannunsu dan haka su nutsu a matsayinsu na matasa shugabannin gobe inda kuma ya bukaci al’umma da ta ci gaba da addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma kuwa yasa a ransa ciwa zai bayyana dukkan wani abu da ya yi a gaba Allah mai kyaune ku mara ku akasin sa a cewar Malam Bashir Othman Tofa Kano.

Ita dai KCCI wato Kano Concerned Citizens Initiatibe kungiya ce da ta hada daukacin Dattawan Kano, Malaman Kano, Yan kasuwar Kano, Yan siyasar Kano, Kungiyoyin Matasan Kano da sauran al’umma maza da mata na al’ummar Kano masu kishi da kuma yunkurin dawo da martabar Kano da kuwacce fuska ta rayuwa inda kuma Bashir Tofa ya nesanta KCCI ta karkata ko nuna goyon bayan ga wata jam’iyyar siyasa a Kano ita dai kungiya ce da aka kafata don ci gaban Kano da magance tabarbarewa da kuma baya na Kano da al’ummarta baki daya inda shugaban kungiyar yan jarida NUJ na Kano Kwamrad Abbas Ibrahim ya yaba wa KCCI Kano nuna kishin Kano ba tare da karkata ga wata jam’iyya ba a matsayin abin Dattako.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: