Abunda yasa Gwamnati bata amfani da kudin da ake karbowa hannun barayin Gwamnati – Ministan Shara’a
DAGA HAUSA TIMES: Antoni Janar na kasa kana Ministan shara’a, Abubakar Malami (SAN) ya dora alhakin rashin yin amfani da kudaden da ake kwatowa hannun barayin Gwamnati da majalisar zartarwa keyi akan yan majalisun kasarnan.
Malami yace akwai kudade da dama da aka karbo amma babu dama Gwamnati ta fara amfani dasu saboda dokar kasa ta hana ta. Yace kuma yan majalisa ne keda hakkin yiwa dokokin kwaskwarima.
Ministan wanda ke bayani bayan wani taron Gwamnonin APC da ya gudana jiya a Birnin Kebbi, yace hakazalika idan an kama masu almundahana an kulle sai alkalai su sakesu wanda wannan ma yana ciwa jama’a tuwo a kwarya
Yace muddin ana son a samu sauyi a irin wadannan abubuwa sai majalisa ta yiwa dokokin gyare-gyare.
Shin kuna ganin ya kamata majalisa ta yiwa dokokin gyara?
Add Comment