Abun Mamaki Game Da Shahararren Mai Kudin Duniya Wato Bill Gate


0 834

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Bill gate shararren mai kudi ne da ya taba kasancewa na daya a jerin masu kudin duniya, wanda har wannan lokaci bana tunanin akwai wanda yafi Bill Gate kudi. Bill Gate ya fara karatunsa a babbar jami’ar nan ta duniya dake kasar Amurka wato Harvard University.

Bayan nasarar kasancewar sa mai kamfanin Microsoft Bill Gate ya bar jami’a ba tare da kammala karatunsa, amma saboda kudinsa da daukakar da Allah yayimasa jami’ar Harvard ta gayyaci Bill Gate yazo yayimusu jawabi a ranat bikin yaye dalibi, wanda kowa yasan wannan jawabi ne da manyan Dr, Professor’s dakuma hazikan daliban jami’a keyi, kuma Bill din yayimusu jawabi, wanda yanzu ina tunanin ya koma ya kammala Bsc dinsa.

Sai dai abun daukar hankali da ban mamaki shine, rayuwar Bill Gate ta banbanta da rayuwar masu kudinmu na Afrika, yi zuwa wannan lokaci akwai kungiyoyi sama 100 da Bill Gate ya tallafa musu kudi, wanda mafi akasarinsu sunfi aiki a kasashenmu na Afrika, dakuma sauran kasashen larabawa dake fama da rashin zaman lafiya.

Akwai manyan kungiyoyi da sukayi fice wurin taimakawa jama’a wanda da sa hannun Bill Gate a ciki, kudin jikinsa yake kashewa domin taimakawa talakawa musulmai, marasa galihu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 8

-Advertisement-

Misali kungiyar UNICEF, wannan kungiya tana tafiya da bangaren taimakon kanannan yara dakuma kulawa da karatunsu a matakin Farko.

Haka kungiyar tana kulawa da lafiyar yara, wanda ta sanadiyar haka ne suka bullo da shirin Pollio, NTD, da sauransu.

Akwai irin hukumar lafiya ta duniya WHO, wanda wannan kungiya ta shahara wurin bincike tare da nemo maganin cututtaka dake addabar jama’a musamman a irin kasashen da shugabannin su sukayi banza dasu, WHO tana daya daga cikin kungiyoyin da suka taka muhimmiyar rawa wurin shawo kan annobar cutar ebola, duk da cewa har yanzu cutar nayiwa jama’ar Liberia barazana, amma WHO tayi kokari sosai.

A Afrika akwai shararrun masu kudi da zasu taimakawa al’umma, amma a nasu tunanin ganin suke kamar idan suna taimko kudinsu karewa zasuyi.

Wannan yasa dukiyar Bill Gate take kara hauhawa shi kafirine idan yayi taimko Allah yana iya musanyamasa abunsa daga duniya.

Allah dai ya kawomuna agajin gaggauwa!

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.