Abun Da Ya Sa Buhari Ya Bai Wa Matarsa Mukami

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sanya uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari mukami da maigidanta ya yi a cikin daya daga cikin kwamitocin yaki da matsalar na ci gaba da jan hankali a tsakanin al’ummar kasar.

A ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya nada mai dakinsa Aisha daya daga cikin mambobin kwamitin.

Malam Garba Shehu shi ne kakakin fadar gwamnati kuma ya shaida wa BBC cewa don an samar da kwamitin ne don magance shaye-shayen muggan magunguna da ke ta karuwa a ksar.

Sai dai fatan mafiya yawan ‘yan kasar shi ne na gannin ayyukan wannan kwamitoci sun kai ga magance matsalar shan abubuwa masu sa maye musamman a tsakanin matasan kasar.

Dalilin zabar Aisha

Malam Garba Shehu ya ce an zabi uwargidan shugaban kasar ta kasance a kwamitin ne saboda ganin irin rawar da take takawa tun farko wajen ganin an yaki shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a kasar.

“Tun ma kafin gwamntai ta zo da wannan batu, ita Hajiya Aisha ta sha tara matan gwamnoni don neman maslaha kan wannan matsala da ta addabi al’umm,” in ji Garba Shehu.

Aisha Buhari

A baya dai matar shugaban kasar ta sha fitowa tana sukarsa a kan abin da ta kira kakagidan da wasu mutane suka yi a mulkin kasar, inda a wata hirar da BBC a shekarar 2016, Hajiya Aisha ta ma nuna cewa ba lallai ne ta goyi bayan mijinta ba idan zai sake tsayawa takara.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

Sannan a makon da ya gabata ma an ta yada wani bidiyo da aka ji maidakin shugaban kasar na cewa, wasu mutum biyu sun mamaye gwamnatin mijin nata su ke cin moriyar komai.

Su waye sauran ‘yan kwamitin?

Tsohon gwamann soja a jihar Legas Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne shugaban kwamitin.

Sannan akwai uwargidan mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo a cikin kwamitin.

Girman matsalar shaye-sheye

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi dai gagrumar matsala ce da ta addabi Najeriya.

Ko a farkon wannan shekarar BBC ta fitar da wani rahoto kan binciken da ta yi a kan matsalar shaye-shaye, inda ta gano hannun wasu kamfanonin sarrafa magunguna.

Hakan ne kuma ya kai ga gwamnatin kasar rufe kamfanonin tare da haramta amfani da sinadarin kodine da ke kara jefa rayuwar matasan kasar cikin hadari.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: