-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Abun Da Nake Gujewa Dr Gumi -Sha`aibu Abdullahi


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abun da nake gujewa Dr Gumi

Daga Shuaibu Abdullahi

Lokacin dana nuna rashin jin dadi na game da yadda Sheikh Ahmad Gumi yake yawan tabo bangaren siyasa daga cikin karatuttukan da yake gabatarwa, da yawa suka mun Chaaa wasu suka dunga zagi na wasu tsinuwa wasu kuwa harda ce mun jahili kawai saboda na fadi raayi na.

Abun mamaki kawai su mutane basu da wata sara sai ta zagin mutane gami da cin mutunci, kawai saboda raayoyin su yasha banban da naka wannan kuma babban kuskure ne.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

- Advertisement -

Daga cikin masu ce mun jahili ko kuma masu mun kallon dan Wuta a kan Malam mafi yawan su gayyar sodi ne bai san su ba bai san wani nasu ba hasalima basa iya biyan kudin mota suje sauraren karatun shi, ni kuma Shiekh masoyi na ne sosai ya temake ni a rayuwa, wato abun da mutane suka kasa ganewa wani zamani muka zo babu yadda zaayi ka shiga shirgin siyasa wani bai zage ka ko yaci maka mutunci ba.

Abun da nake gudu kada ya faru da malam shine ya dunga faruwa wanda hakan yasa na shiga damuwa matuka, ya zamanto cewa cikin masu zagin Malam harda yan Daudu dama wadanda ko Alwala basu iya ba.

Wannan na daga cikin dalilin daya saka na koma baya na jawo alkalamina na rubuta tarihin Malam mai cike da abun alfahari, duk da haka ina mai jan hankalin Malam ya duba Girman Allah ya fita shirgin Siyasa, muna jin bakin ciki idan aka zage shi; Allah ya kara gira ya kuma jikan Baba

Ni ina yima kowa fatan alkairi kuma duk wanda ya zage ni banji haushi ba kuma na yafe masa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: