Abubuwa 5 da baku sani ba game da matashi mawakin hausa hip hop – Lil Ameer

65

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

Hakika masana’antar nishatarwa ta Arewa tayi babban rashi da rasuwar dan matashi mawakin hausa hip hop, amma indai ajalin mutum ya kai babu wanda zai iya kubutar dashi.

Ameer Isa Hassan ya rasu ranar 14 ga watan Satumba a garin Kano sanadiyar hatsarin mota. Anyi jana’izar shi ranar juma’a a layin massalacin juma’a na tarauni.

ga wandada basu san labarin wannan matashin ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani;

1. Haifafan Dan jihar kano ne

An haifi marigayi Ameer a cikin 2003 a jihar Kano

2. Har zuwa lokacin rasuwar sa mawakin yana koyan darasi a makaranta

Duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalin shi wajen koyan darasi. ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi yaje na islamiyya. sai karshen mako yake samun damar yin aikin waka. babban burin marigayi shine in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama.

Marigayi Lil Ameer Tare Da Mahaifiyarsa

3. Iyayen sa sun mara mai baya

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 404

hakika iyayen suka bashi damar fara waka kuma uwar take taimaka masa wajen rubuta wakokin.

Ameer ya canza makarantu domin masoyan sa sukan tunkare shi idan yana koyan darasi.

4. Ya fara waka tun yana jjs 1 na makarantar sekandare

matashin ya fara waka ne domin tun yana dan karami yake muradin waka. ya fara waka ne domin ya nuna ma duniya cewa matasa daga yankin arewaci kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.

5. Yayi wakoki da dama kuma yayi wasa tare da sauran shaharren mawaka

cikin wakokin da marigayi yayi akwai “boss”, “champion”, “ilimin boko da addinin musulunci”, “dance for me” da dai sauran su.

Matashin wadda ake wa lakabi “karaminsu babbansu” yayi waka tare da shaharraru da dama kuma yayi wassanni da dama a wurare daban-daban#

Lil Ameer Tare Da Classiq

Allah ya jikanshi da rahama, Ameen

 

Souce In Pulse.Ng

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.