Tsohon Gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima ya nuna kaduwa da kuma alhininsa kan kisan rashin Imanin da aka yi a Zabarmari a karshen makon jiya.
Sanatan Wanda take tare da tawagar ‘yan majalisar tarayya na jihar da suka kunshi Sanata Ali Ndume da sauran ‘yan majalisar tarayya sun ziyarci jihar ne domin jajantawa Gwamnatin jihar da kuma mutanan Zabarmari.
Kashim Shettima ya nuna kaduwa Alan wannan kisan rashin Imanin da aka yi musu.