Labarai

Abin Takaici Yadda Ake Mai Da Mutane Kamar Dabbobi A America

KARE HAKKIN DAN ADAM…

Wannan abunda kuke ga ni mai kama da Kejin ajiye Kaji Mutane ne a ciki ba Kaji ba ne ko Dabbobi

Kuma wani abu da zai baku mamaki shi ne, wai a Kasar da suke ikirari kuma suke cika baki da sunfi kowace Kasa cigaba a Duniya.

 

Abin takaichi anan ne a ke yiwa Mutane haka kamar Dabbobi wato Kasar America.

Idan ka tashi tsaye ko ka kwanta ,wan nan ragar da kuke gani an hadata da Wutar Lantarki mai karfin gaske,kana tabawa ko kuma ki ta yaya jikin ka ya taba ragar sai ta ja Jininka kaji wani mugun shoking kamar ranka zai fita.

Toh dan Allah Jama’a wane irin Cigaba ne ake nunawa a Kasar America ?

Karshe wannan Cigaba ne ko kuma Cibaya ko kuma me za a kira irin wan nan Danyan Aiki da rashin tausayi da ake yi wa da adam?

Allah ya kiyaye mu daga fadawa kunchi da masifar rayuwa ameen

Daga: Tukuntawa24