Kannywood

Abin da Ya Sa Ba a Gani Na a Harkar fimm, – Maryam Booth

Tsawon lokaci dai a yanzu fitacciyar jaruma Maryam Booth, ta yi batan dabo, a cikin harkar fim, harkar da aka san da ita ce ta yi suna, har duniya ta san ta.

Tun bayan bullar Video na tsaraicin ta da wani saurayin ta ya yada, jarumar ta dauka matakin killa ce kanta, wanda hakan ya sa ba kowa ya ke ganin ta ba, sai dai kawai a gan ta a hotunan tallukan da ta ke yi wa kamfanoni.

Bayyanar farko da ta fara yi tun daga wancan lokacin dai ita ce, a lokacin Mutuwar Mahaifiyar ta, kimanin wata biyu da suka wuce, a nan ne kowa ya ganta a wajen zaman makoki a Kano tana karbar gaisuwa, bayan wannan kuma ba a sake ganin ta ba.

A lokacin addu’ar kwana 40 da rasuwar Mahaifiyar ta, sun hadu da wakilin Jaridar Dimukaradiyya a Kano, inda ya tambaye ta a game da rashin ganin ta da ba a yi a yanzu.

Sai ta ce “Gaskiya tsawon lokaci tun bayan abin da ya faru wanda saurayin da muke soyayya da shi a baya ya yi mun, na sakin hotona, sai na dauki matakin boye kaina, duk da na san kaddara ce ta same ni, amma dai abin ya taba rayuwa ta, don ko a fim ba na fitowa, sai na koma ina yin harkokin kasuwa na, wanda na ke yi da bai shafi harkar fim ba, don haka sai ya zama ba na gani na. ”

Ta ce gaba da cewar “A yanzu kuma bayan rasuwar Mahaifiyar mu to abubuwa sun kasa sauya mun, don haka sai na shiga wata Sabuwar rayuwa ta maraicin rashin uwa, wannan ya sa ni da kanena Amude muka koma Abuja da zama.” a cewar ta.

“ko yanzu ma da muka hadu na zo ne don yin addu’ar kwana 40 da rasuwar ta, amma dai a yanzu ina Abuja da zama, daman ita ce take kula da mu kuma Allah ya yi mata rasuwa, don haka ina cikin jimamin maraicin rashin Mahaifiya ta wannan ya sa Rayuwa ta sauya a gare ni” inji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: