Abin da El-Rufai ya keyi kan maganar Ilimi a Kaduna abu ne mai kyau – Buhari

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kan gyaran da ya ke yi a fannin Ilimin jihar.

Buhari ya fadi haka ne a taron farfado da harkar ilimi a kasar nan da ya halarta a safiyar litinin a dakin taro dake fadar gwamnati.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 16

Buhari yace tabarbarewar Ilimi a kasar nan abu ne da yake ci wa gwamnati tuwo a kwarya kuma ya zama dole a dawo daga rakiyar nuna halin ko-in-kula da akeyi don samar wa fannin mafita na dindindin.

Ya ce abin da gwamnan Kaduna yake yi a Kaduna abu ne mai kyau domin babu yadda za ace wai malami ya kasa cin jarabawar abin da zai karantar wa dalibi.

Ya bada labarin wani abokinsa dan Najeriya da ya dawo makarantar firamaren da ya yi a da domin tallafa musu amma abin da ya bashi mamaki shine ya kasa bambamce tsakanin malamai da dalibai saboda lalacewar ilimi da muka fada ciki a kasar nan

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.