Abdullahi Shehu Gatan Matasa Da Yara Marasa Galihu A Jihar Sokoto


0 1,094

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Aliyu Ahmad

Dan kwallon Nijeriya mai wasa a kungiyar Bursaspor dake kasar Turkiya, Abdullahi Shehu ya kasance abin koyi ga duk wani matashi dake da ikon tallafawa al’umma.

A halin yanzu Shehu ya kasance garkuwa ga matasa a jiharsa ta Sokoto, inda yake fadi tashi ba dare ba rana don ganin ya yaki zaman banza da harkar shaye-shaye ga matasa. Sannan kuma ya kasance baya goya marayu.

Idan masu karatu za su iya tunawa, Shehu tare da hadin gwiwar takwaransa Ahmed Musa, a azumin da ya gabata sun tallafawa marasa karfi da dama a jihohin Kano da Sokoto. Ta hanyar raba kayan abinci, kayan sawa, gudummawar kudi da sauransu.

A wannan karon ma, matasan ba su yi kasa a gwiwa ba a irin ayyukan alkairan da suka saba yi wa al’umma, inda a makon da ya gabata suka raba kayan makaranta ga yara dalibai, wadanda suka hada da littafai, alkalami da sauransu da dama.

Haka kuma ya dauki nauyin biyan kudin makarantun matasa da yara marasa galihu da dama a fadin jihar Sokoto a kwanan nan.
Baya ga haka kuma ya jagoranci gudanar da gasar kwallon kafa a tsakanin kananan hukumomi 23 dake jihar, wanda dan kwallo Shehu ya dauki nauyi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

- Advertisement -

Gasar wadda aka yi lakabi da ‘Sokoto State Governors Cup’, an dauki kusan tsawon wata guda ana buga shi.

A yayin zantawar Shehu da RARIYA, ya bayyana cewa dukkanin kayayyakin da za a yi amfani da su a gasar, kama daga jasi, kwallaye da sauransu ya sayo su ne daga kasar Turkiya.

Shehu ya ce ya yi hakan ne domin ganin ya hada kan matasan jihar Sokoto musamman na kananan hukumomin dake gefe. Wanda yin hakan zai sa su shigo gari ana damawa da su.

Baya ga haka, Shehu ya kafa Gidauniya domin yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa. Inda Gidauniyar za ta dinga shiga lungu da sakunan jihar Sokoto domin wayar da kan matasa game da illar shaye-shaye.

Haka kuma gwamnatin Sokoto ta sha alwashin samawa Shehu katafaren fili, inda zai gina cibiyar harkar wasannin da makamantansu, wanda hakan zai yi silar samun ayyukan yi ga dubban matasa a jihar Sokoto.

Babu shakka Shehu ya zama abin a yaba masa bisa irin wannan namijin kokari da yake yi domin ganin ya tallafawa matasa ‘yan uwansa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.