-Advertisement-


Aban Hakuri Ko Na Dauki Mataki Cewar Deezell


0 1,138

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fitaccen mawakin Gambara na hip-hop, Ibrahim Rufa’i Balarabe (Deezell), ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewar shi ne ya saki hoton bidiyon nan na tsaraicin Maryam Booth.

A wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Twitter da Instagram, Deezell ya ce, “An jawo hankali na ga wani bidiyon tsaraici na jarumar Hausa Maryam Booth wanda ke yawo a kafofin soshiyal midiya tare da kazafin cewa wai ni ne na saki bidiyon. Sai dai kuma abun bakin ciki shi ne su wadannan masu mugun nufin, wadanda wakilan jawo bala’i ne, sun kasa kawo duk wata shaida ko hujjojin cewa ni din ne wanda ya saki bidiyon da ke yawon. Ina so in bayyana karara cewa ba ni ba ne wanda ya saki bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, kuma a gaskiya a iya sa ni na ban san wanda ya sake shi ba. Kuma a matsayi na Musulmi, na sa ni cewa ya sabawa Alkur’ani mai tsarki da koyarwar Annabin mu Muhammadu (tsira da aminci su tabbata a gare shi) mutum ya yada ko ya saki abun da bai dace ba na wani mutum a bainar jama’a, musamman a soshiyal midiya, da nufin musguna masa”. Inji Deezell.

Ya ci gaba da cewa “Haka kuma wannan mugun zargin da a ke yi min na yada tsiraicin ‘yar uwa ta Musulma gaba daya karya ne ta kowace fuska, kuma ina so kowa ya sa ni cewa wadannan zarge-zargen duk karya ne. Ko da yake ban san dalilin da ya sa a ke yi min wannan zargin ba, ina kira ga wadanda ke yada wannan kazafin da su janye maganar su, kuma su ba ni hakuri cikin awa 12 ta hanyar soshiyal midiya ba tare da bata lokaci ba. A cewar Deezeel.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai soshiyal midiya ta cika da kwakwazo kan bullar wani guntun bidiyo na fitacciyar jarumar ta Kannywood inda a ka gan ta tsirara a wani daki, ta na kokarin kwace wayar da wani ko wata ke daukar ta.

A nan ne kuma sai wasu su ka rika yada zargin cewar wai fitaccen mawaki Deezell ne musabbabin shigar bidiyon a kafafen yada zumunta na zamani. Mujallar Fim ta bada labarin cewar, jami’an tsaro na farautar wasu matasa biyu, mace da namiji, wadanda a ke zargi da sakin hoton bidiyon, ta bakin shugaban kungiyar jaruman fim reshen Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, A cewar sa “Matasan sun shafe shekaru uku su na karbar kudin toshiyar baki daga hannun Maryam tare da barazanar cewa za su saki bidiyon a gari idan har ta daina ba su kudi”. Inji Alhassan.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Sai dai kuma wasu kafofin soshiyal midiya su ka baza labarin cewa wai shi Deezell din ne ya saki bidiyon.

Guda daga cikin kafofin, akwai ‘Hausa Loaded’, ta bada labarin cewa wai Deezell ya yi soyayya da Maryam a tsakanin 2016 da 2017, amma su ka bata.

Kafar ta ce, da su ka bata sai ya dauki hayar wata yarinya domin ta samo masa hoton Maryam Booth tsirara, abun da yarinyar ta aikata. Bayan ya samu hoton sai ya rinka neman kudi a wajen Maryam tare da barazanar idan ta hana shi zai dau mataki.

Kafar ta kara da cewa, a shekarar nan da ta gabata ta 2019 Maryam ta yi wa kamfanin Ajino-moto talla, a ka biya ta Naira miliyan 25. A nan ne mawakin ya bukaci ta ba shi Naira miliyan 10 daga ciki, ita kuma ta fada masa ba ta da irin wannan kudin, dalilin haka ne ya fara tura wa abokan sa bidiyon.

To amma dai Deezell ya ce “Wannan labari duk zuki-ta-malle ce. Idan su ka ki kuwa, babu abun da zai rage min illa in dauki matakin shari’a da su domin in kare mutunci na da na sha wahala na samu. A karshe, ina tausaya wa wadda wannan ibtila’i ya fadawa tare da yin kira a gare ta da ta binciki wanda ya saki bidiyon da ke yawo, kuma ta dauki mataki shari’a da ya dace a kan wadanda su ka aikata mata hakan”. Inji Deezell

#Northflix

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.