Labarai

A Yau Jumma,a Jahar Kebbi Ta Bi Sahun Jahohin Da Suka Yi Wa Buhari Addu’a

Gwamnantin jahar Kebbi a karkashin jagorancin gwamna Abubakar Atiku Bagudu ta shirya taron addu’o’i na musamman ga shugaba Muhammadu Bubari, kamar yadda wasu jahohin arewacin Nijeriya suka yi.

Taron wanda aka yi a masallacin idin birnin Kebbi ya samu halartar daruruwan mutane, kama daga ‘yan kasuwa zuwa ‘yan siyasa, da malaman addinin, da sarakunan gargajiya da sauransu.
Ga hotuna daga wajen taron addu’ar: