A T Ahmad Mu`azzu Ya Zama Mukaddashi Shugaban Hukumar INEC

0 121

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Cikakken Dan Jihar Gombe Ya Zama muƙaddashin Shugaban Hukumar INEC ta ƙasa Wato Air Vice Marshal A T Ahamed Mu’azu

A Yayin da ake jiran sake tantancewar nada Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Ahamed Mu’azu ya zama muƙaddashin Shugaban hukumar a Jiya litinin.

Farfesa Mahmood Ya mika wa Ahmed Mu’azu (rtd), ragamar shugabancin hukumar a matsayin Shugaban riko, har sai Majalisar Dattawa ta gama tantance shi kafin a sake Naɗa shi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

In baku manta ba Yakubu ya cika shekaru biyar yana aiki ranar Litinin. Wanda Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada shi a watan Nuwamba na shekarar 2015.

A nasa martanin, Mukaddashin Shugaban Hukumar, Ahmed Mu’azu (rtd), ya gode wa shugaban INEC mai barin gado da abokan aikinsa bisa ga dama da kwarin gwiwar da suka ba shi na kula da hukumar.

A ƙarshe Ya ba da tabbacin cewa zai kula da lamuran hukumar tare da yin duk abin da ya kamata.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: