Kannywood

A Shirye Nake Na Sake Komawa Gidan Miji Karo Na Uku, Inji Adaman Kamaye

A cigaba da kawo muku tattauawar da Wakiliyarmu RABI’A SIDI B. ta yi da tauraruwa a shirin nan na ‘Kwana Casa’in’ wato ZAHRA’U SALE FANTAMI wadda aka fi sani da ADAMAN KAMAYE, a wannan makon ta tabo al’ummarra da dama wadanda suka shafi rayuwarta na aure, inda ta ce, ta taba aure karo biyu, tana kuma da yara uku.

Sai dai a halin yanzu bata da miji, kuma a shirye take ta aure duk wanda zai kare mata mutuncinta ya kuma bata ci da sha daidai gargwado, ga dai yadda hirra ta kasance:

Ya kike iya hada kasuwancinki da kuma harkar sana’arki ta film?

Kamar shi kasuwancina Hajjiya ba mai tsanani bane kuma me tsanani ne, domin an ce ka nemi duniya kamar ba za ka barta ba ko, kuma an ce ka nemi lahira kamar kana can. Toh! wannan sana’ar tawa dadin da take mun ai tare na ke da ita a jikina, Tunda kayan nan suna cikin mota kuma ko da yaushe in dai ba akasi aka samu ba motan nan da ita zan fita, da kwastum da komai da kika dani na birni dana kauye duk akwai a cikin mota ta, duk wani abu da kika sani ya shafi harkar dirama, toh ina ajjiye da shi a cikin mota ta, da an ce mun ‘Hello’ Adama kina ina? ko Haj. Zahra kina ina?, musamman ina cikin garin Kanon ina wuri kaza dan Allah za mu yi aiki da ke wuri kaza, toh ballantana ma harkar mu ta fim din muna da tsari ai, in zan yi aiki da ke kamar gobe ko jibi toh tun shekaran jiya waccen zan kira ki “Ah! Dan Allah Haj.Rabi’a jibi kina da abun yi ne?” “A’a! ba ni da abin yin” “Dan Allah za mu dan yi rekodin da ke a wuri ka za, lokaci ka za, da karfe ka za” Toh! kinga shadul na hannuna na san da wannan aiki.

Yanzu kamar hirar nan da muke da ke a yanzu ai gobe laraba kinga ina da aiki na wani yaro ana ce masa Ishak Mia, ya zo tun shekaran jiya yau kwana biyar da ya biyo ni da kudina da ‘Script’ dina har gida, to kinga gobe laraba gobe ne shedul din aikinsa, kuma in Allah ya kaimu zan je in masa aikinsa. Toh! kinga babu wani tsanani a ciki ko da ba a gari kake ba in an sanar da kai abinda za ka yi za ka garzayo ka dawo tunda ka ji ka gani.

 

Ya Batun Aure Fa, Shin Kin Taba Yi?

 

Na yi aure ina da yara kuma ina tare da yarana, muna rayuwa tare, na yi daya na fito, kuma na kara yin daya duk na haihu, sannan ina da ‘ya’yana Allah ya ba ni su, na yi tagwayena Hassana da Hussaina na aurar da su, su ne ‘yan matan ana kiran daya Fa’iza ana kiran dayar Farida, sannan da autarsu ita ce Gambo wato Rabi’a amma ba babansu daya ba.

 

Ko kina da shirin sake yin wani auren a yanzu ko kuwa tukunna dai?

 

Ba ni da aure a halin yanzu sai dai niyya, ina so zan yi aure, idan ubangiji Allah ya kawo mun miji na gari zan yi aure. Toh! amma kin san su Maza har kullum basa yi wa Mata adalci wani lokaci kuma Matan ne basa yi wa kansu adalci, toh amma ina so duk wani mai kaunata da masoyana su tayani da addu’a, Ubangiji Allah ya ba ni miji na gari wanda za mu zauna lafiya da ni da shi, ina da niyya kullum cikin niyya nake, amma dai har yanzu ban dace da kalar wanda zan aura ba mu zauna da shi din bane sai dai ana nan ana lalube, kuma ana bawa Allah zabi ya zaba mana abinda ya fi alkhairi, dan aure ai ba zai ki aure ba mun gada aure kam!, dan sunna ai baya gudun sunna muna cikin niyya.

 

Wanne irin Namiji kike so?

 

Hajjiya Rabi’a kenan, Namijin da nake so na aura?, wallahi na gari mai tsoron Allah da addini, wanda zai tsara hakkin musulunci, ba son zuciyata ba, wanda za mu zauna lafiya, wanda ya san hakkin aure, wanda zai ban ci da sha da tufafi, ya kula da ni ya kula da rayuwata, shi nake so.

 

Misali wani a cikin masana’antar kannywood ya fito ya ce yana sonki zai aureki shin za ki amince ki aureshi ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?

 

Kina jina ko? ni in ma ba a cikin masana’antar Kannywood yake ba, ko daga karkashin kasa ya fito indai ya tsara wadannan hakkunan da nake nema toh zan iya aurensa kuma zan iya zama da shi, [Dariya] ko wanne iri ne in a daga ina yake ya zamo me tsoron Allah ne, wanda ya san hakkin aure, ba kowa ne kin san ya san hakkin aure ba, yara ga su nan

 

Wanne abinci kika fi so?

 

Abincin da na fi sha’awa a duniya Tuwon Dawa ko na Masara, yadda kika ganni ni ‘yar kauye ce tifikal, idan na samu tuwo miyar kuka ni magana ta kare an yi hajji da umara, dan haka mutane da suke so su kawo kansu su ce suna so su aure mu suke tsoranmu ko suke gani muna zuba musu a ruwa ko suna ganin kamar mun fi karfinsu toh babu wannan wallahi, mu masu saukin kai ne, kar su dauka ko muna da damuwa, ko wani son kai ko wani kyashi, ko wani jiji da kai na rayuwa dan Allah ya baka wata daukaka ko ya kawo maka wata dama, a’a mu ba haka muke ba gaskiya, duk wanda ya zo za mu yi maraba da shi kuma duk wanda yake son mu muna son shi, dai-dai gwargwado kuma muna intatemin din masoya domin in sun tare mu sai ka kiyaye duniya ta zama abin tsoro, bama sakin jikin mu amma kuma za mu yi intatemin dinsu ta yadda ba za su ji haushin mu ba ko su tafi suna zagin mu. Saboda akwai wanda in ka yi musu magana ma zai yi inbarazin dinka su wulakantaka, toh ni dai ba na haka, duk yadda zan yi in yi intatemen din masoyina na sani zan masa dai yadda ba zai ji haushina ba mu rabu lafiya, amma kuma bana sakin jiki, ba ko ina nake sakin jiki ba saboda yanzu rayuwar ta zamo sai ka bawa kanka tsaro, toh wannan shi ne, a matsayina ta Adaman kamaye ko in ce Zahra’u Sale, ko Uwar Magaji ko ta me sittin goma, duk sunana ne.

Wasu na ganinki a dadin kowa tare da kamaye kuma suna nuna sha’awar dacewar aurenku me za ki ce a kan hakan?

Ni kamaye ubana ne ba maganar aure tsakanina da shi dukkansu ma da shi da Malam Nata’ala ba ni da wani miji a cikinsu, dan duk wanda na zo da mijin na kamo hannunsa ba wanda ba zaimin alolanci ba, na farko dai Dan Azumi Baban nan kin sani tsohon marubuci ne kuma darakta ne kuma furodusa ne, ya dade yana wallafa littattafan Hausa, in wani bai sanshi ba wani ya san shi Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa, tun kan na san zan zo wannan masana’anta ko na ce tun ba ni da wayo ma ya ke wannan masana’anta, in a layin masana’antar Kannywood ne kinga Kakana ne, ni tattaba kunnenshi ce. Shi kuma Malam Nata’Ala a layin masana’antar ‘Kannywood’ shi kuma kakana ne, tunda tun ana wasan dabe da su Ibro Rabilu Musa Allah ya ji kansa suke wasa da na kundubu babu wanda bai san Na kundubu ba, toh! tsakanina da su kawai wasa ne da dirama, in mun hadu a wurin wasa mu mutunta junanmu mu gaisa inda shawara wacce za mu yiwa juna ta karuwa mu yi, inda wani wani alkhairi da ya taso za mu je mu karu da shi mu hada kanmu mu tafi, amma maganar aure babu ita ko makamanciyar haka wannan magana sai in ce kamar an yi haramun ma dai dan babu wannan layin, tunda da ba zai auri ubansa ba, ko ba gaskiya ba? ni duk iyayena ne wadannan ba aure tsakanina da su har gaba da abada. Yanzu kin ga akwai wani hoto inda ya mikamin ruwan nan na turo miki, tallan gidan hoto kawai muka je mu kai aka rinka cewa mun yi ‘Pic Wedding’ toh! kin ga irin wannan rudanin duk babu shi gwara ma kowa ya sani uba ne a wurina ko yanzu in ina da abinda ya shige mun duhu ko ya dameni zan kirawo shi ko in je gida in same shi in zauna in ce ka ji – ka ji baba dan azumi, zai ce to ki yi ka za- ki yi ka za in kikai haka kikai haka zai yi, zai dai kawo shawarwarin da zai zamemun mafuta shi ne kawai.

Za mu cigaba a mako mai zuwa. 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: