Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fito fili ya yarda da cewa akwai baraka tsakanin sa da tsohon gwamnan jahar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya ce a shirye yake da su shirya.
Yayin da yake magana da manema labarai a ofishinsa, gwamnan ya ce sun yi zaman mutunci da Kwankwaso kuma abokinsa ne na tsahon lokaci.
Rikicin manyan jiga jigan siyasar guda biyu dai ya haifar da kafuwar bangarori biyu a Jam’iyyar APC ta jahar Kano, wanda ake kira Kwankwasiyya da Gandujiyya.
A kwana kwanan nan, gwamnan jahar Katsina, Aminu Masari ya bayyana cewa suna yin wani yunkuri na shirya ‘yan siyasar biyu, domin a fadarsa, su gwamnonin Arewa basu jin dadin abunda ke faruwa.
Ganduje dai ya ce kofarsa a bude take na yin sulhu.
Add Comment