Labarai

A Sallami ‘Yan Wasa Uku Ko Ni Na Tafi – Messi

Jaridar Daily Express ta rawaito cewa Lionel Messi ya ce ba zai sabunta kwantiraginsa da kungiyar ba in har ba ta sallami wasu ‘yan wasa uku ba
MESSI SNUBBED.jpg
Sunayen da Messi ya jero a sallama sun hada da Jeremy Mathieu, Andre Gomes da Lucas Digne da Messi ya nuna ba sa tabuka komai wajen taimakawa kungiyar samun nasara a wasanninta
Rahoton ya bayyana cewa Messi ya ce yana da bukatar kungiyar da ta sauya Luis Enrique a matsayin mai horas da ‘yan wasan kungiyar a karshen kakar bana