-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

A Kwai Mugun Nufi A Sakin Bidiyon Ganduje –Inji Fadar Shugaban Kasa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fadar shugaban Najeriya ta nuna cewa, akwai mugun nufi na siyasa a yanayin yadda a ka fitar da bidiyon da a ke zargin gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana a cikinsa ya na karbar cin hanci daga ’yan kwangila da masu bada rahoton su ka rufa wa asiri ta hanyar boye sunansu tare da tona asirin gwamnan.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na fadar shugaban kasa kuma babban lauya mai mukamin SAN, Farfesa Itse Sagay, a hirarsa da jaridar Punch.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa, a hakikanin gaskiya har yanzu masu zargin gwamnan ba su gamsar da shi cewa ba su da wani mugun nufi a cikin badakalar ba.

“A wajena lamarin ya na cike da sarkakiya da harshen damo kuma ya na kunshe da alamun mugun nufi a cikinsa tare da hadin baki irin na siyasa wanda masu adawa da gwamnan su ka kitsa. Don haka mu na bukatar wani abu sahihi fiye da wanda mu ke gani a halin yanzu kewaye da batun,” in ji Farfesa Sagay.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Don haka sai farfesan ya jaddada cewa, “don kawai wani a soshiyal midiya, wacce ke cike da karairayi da nuna tsana ya zargi wani da aikata laifi, hakan ba ya nufin wannan zargi ya zama gaskiya nan take.

“Ni a kashin kaina ta fuskar ilimin sanin shari’a zan so a ce ’yan kwangilar su fito su bayyana kansu su ce su ne su ka bayar da cin hancin tukunna, amma har yanzu hakan ba ta faru ba. To, ko ma dai mene ne duk lokacin da cikakken binciken ya taso, mu na da hukumar da a ka kafa don yaki da cin hanci da rashawa, wacce ta na da kwarewar da za ta iya gano gaskiyar komai ko akasin hakan, wato EFCC kenan na ke nufi.”

Ya kara da cewa, duk lokacin da ta tabbata cewa akwai zargi mai karfi a kan wani mutum hukumar za ta yi wani abu a kai, kamar yadda ya faru a kan Gwamna Fayose ko Misuliu Obanikoro, wadanda komai ya bayyana a fayyace ba irin wannan badakalar ta Ganduje ba.

“A nasu lamarin an ga yadda a ka zuba kudi masu yawa a cikin asusun banki, amma

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: