Labarai

A kawo mana ɗauki kan yadda ɓata gari ke far mana – Al’ummar Ɗorayi

A kawo mana ɗauki kan yadda ɓata gari ke far mana – Al’ummar Ɗorayi

 

Al’ummar unguwar Ɗorayi Ƙonannen gidan Mai dake yankin karamar hukumar Gwale, sun nemi ɗaukin mahukunta bisa yadda wasu matasa ke farwa mutane da makamai a yankin.

 

A zantawar wasu daga cikin matasan unguwar da Wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, sun ce ko a ranar Larabar nan sai da wasu rukunin matasa sama da ɗari uku suka shiga yankin na su tare da farwa mutane da makamai.

 

Mutanen unguwar ta Ɗorayi ƙarama Ƙonannen gidan Mai, sun kuma nemi ɗaukin mahukunta da a tallafa musu wajen gina musu ofishin ƴan sanda, domin zai taimaka wajen kawar da ayyukan ɓata garin.