A Karon Farko Kwararrun Likitoci Daga Kasar Waje Sun Zo Duba Lafiyar Shaikh Zakzaky


0 130

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Bilya Hamza Dass

Bayan zaman sauraron karar da Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar akan Shaikh Zakzaky, Alkalin Kotun ya bada umurni ga hukumar DSS suyi hanzarin gayyato Kwararrun Likitotci daga kasar waje domin duba lafiyar Malamin tare da me dakin shi Malama Zeenah wadanda suke fama da munanan raunuka jikinsu sanadiyar harbi, kaman yanda lauyan Shaik Zakzaky Femi Falana ya bayyana ga alkalin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Yau Alhamis Lauyoyin sun samu shigowa Nijeriya karkashin Hukumar Kare Hakkin Bil’adama na Islama IHRC inda suka gana da Malamin tare da Matarsa a wajan da ake tsare dasu domin duba yanayin jikin nasu. Malami ne yana tsare ne sama shekara 3 tin bayam abinda yafaru tsakaninsu da runudunar sojan kasar a Watan Disambar 2015 a Zariya.

Cikin kwanakin nan de mabiyan Shaikh Zakzaky sun matsa lamba kan yanayin lafiyar nashi inda suke ta shirya taruka da manyan-manyan Zanga-zanga a fadin kasar nan musamman Abuja.

Hoto: Shakh Zakzaky tare da matarsa Malama Zeenah, daga baya kuma tawagan likitocin ne.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.