Daga Comr Abba Sani Pantami
Wani tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Abu Ibrahim, ya ce Nijeriya za ta zauna lafiya a karkashin Asiwaju Bola Tinubu, idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa a zaben 2023.
Tsohon sanatan dan asalin jihar Katsina ya yi wannan maganan ne a karshen mako a Abuja yayin kaddamar da kungiyar nuna goyon bayan Bola Tinubu (BTSO), The Nation ta ruwaito.
Ya nuna goyon baya ga masu tallata shugabancin Bola Tinubu a 2023, yana mai cewa ya san Shugaban na APC na Kasa sama da shekaru 20.
Ibrahim ya bayyana Asiwaju Tinubu a matsayin dan Najeriyar da ke da manufa kuma babban jagora wanda ke da sha’awar gano kwarewa da kwazon matasa masu tasowa ya jagorance su zuwa mukamai.