Labarai

A Bayyane Yake Mulkin Nijeriya Ya Fi Karfin Dattijo Mai Shekara 62, In Ji el-Rufai

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna, ya bayyana cewa, ba shi da sha’awar shugabanci a 2023 saboda ya tsufa, don haka a bar wa matasa takarar domin su bayar da tasu gudunmawar.

Gwamnan mai shekaru 62 ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC a Kaduna.

El-Rufai, wanda har yanzu bai kammala wa’adin mulkinsa na biyu ba, ya ce, tuni shekaru sun fara bayyana a jikinsa.

Ya kara da cewa, “gudanar da mulkin Nijeriya babban aiki ne, wanda a bayyane yake ya fi karfin mutum dan shekaru 62 da haihuwa. Duba ni, kalli furfura ta. Idan kaga hoto na lokacin da aka rantsar dani, gashi na duka baki ne, amma duba yadda ya zama yanzu.”

“Wannan aiki ne mai matukar wahala kuma a hakan mulkin jiha daya ne kawai, to yi tunanin 36. Aiki ne mai wahala, balatana ace Nijeriya gaba daya,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko yana da sha’awar mukamin Mataimakin Shugaban kasa, sai ya ce, “Ban yi tunanin hakan ba kwata-kwata. Na fada cewa a tsarin siyasar da muke da shi, bayan shekaru takwas na Shugaba Buhari, shugabancin kasa ya tafi kudu.

El-Rufai ya ce, ya gaji da alakanta shi da fadar shugaban kasa, ya kara da cewa, hakan na faruwa a cikin shekaru 15 da suka gabata.

“Na kasance ina fama da wannan zato na son takarar shugaban kasa tun a shekarar 2006, na sha wahala tsawon shekaru 15 a yau, kuma ina rashin lafiya kuma na gaji da shi. Akwai mutanen da suke shirin zana ni a wani hoto domin in fita takarar shugaban aasa, amma ba su san cewa ba sha’awar wani mulki ba daga wannan.”

A kan wadanda suka kira shi da dan Jihadi, ya ce:, “Sun kira ni da kowane irin suna, sai suka ce ni bahaushe ne ba-Hausa-Fulani, ni dan Jihadi ne da duk wannan, a yaushe na yi Jahadi? A Ina? Ni ban ma kasance mamba a cikin wata kungiyar Musulunci ba.”

“Ni Musulmi ne, eh, mai kwazo, amma na yi imani addini na sirri ne. Ko a nan ofis din nan, idan lokacin sallah ya yi, sai dai kawai in ba da uzuri kamar zan tafi bandaki, ban nemi kowa ya zo ya yi sallah tare da ni ba, domin duk za mu je kabarinmu daban.”

Ya ce, “Ku duba kusa da ni ku gani, ba Musulmai ne kawai suka kewaye ni ba, wannan gwamnatin ita ce kadai gwamnatin jiha a kasar nan da ke da akalla mutane daga wasu jihohi 13 na tarayyar a matsayin mambobin majalisar ministoci.”

“Daya daga cikin masu fada a ji a rayuwata, daya daga cikin makusanta na na siyasa shi ne, Fasto Tunde Bakare. Fasto Tunde Bakare ne ya gabatar da ni ga Buhari da CPC (Congress for Progressibe Change). Ban shiga CPC ba saboda Buhari yana zaune a Kaduna ko kuma don ni dan arewa ne. Don haka, idan ni dan Jihadi ne na Islama, me zai sa Fasto Tunde Bakare ya yi magana da ni?”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: