Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa gwamnonin jihohin arewa 19 sun soma tattara kudi da zasuyi amfani da shi wajen sake farfado alámuran yankin da suka hada da bankin arewa (Bank of the North).
Ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawa da yan majalisar zantarwa na jihar Kano, ya kuma kara da cewa gwamnonin sun yarda da akan a taron da suka gudanar a jihar Kaduna.
gwamna Ganduje ya kara da cewa gwamnonin sun amince da farfado da manya-manyan masana’antu da suka rushe a yankin arewacin kasar musamman na masaka.
Haka zalika yace sauran batutuwan da suka zanta a taron sun hada da wanzar da zaman lafiya da kuma kawo karshen rikicin makiyaya tare da manoma a yankin.
Daga karshe Ganduje ya sa hannu akan wasu dokokin da aka gyara wanda ya hada da dokar jami’ar kimiya da fasaha na jihar Kano da na jami’ar arewa maso yamma.
Za mu daidaita al'amuran Arewa – Inji Gwamnonin Arewa 19

Add Comment