2019: Ya Kamata Matasan Kumbotso Su Sakawa Ballah -Mahmud Girma

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Tsohon Dan takarar majalisar dokoki a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Honarabul Mahmud Tijjani Suraj (Girma) ya yi kira da matasa qaramar hukumarsu da su goyawa Dan takarar majalisar tarayayya karkashin tutur jam’iyyar PDP, Honarabul Ibrahim Umar Ballah a takarar da yake yi a zabe mai zuwa.

Hon Girma ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a jihar Kano, inda ya ce lokaci ya yi da matasa da kuma al’ummar Kumbotso za su sakawa dansu, wanda ya yi aiki tuquru lokacin da ya wakilce su a majalisar tarayya daga 2007 zuwa 2011.

Talla

Ya ce tsarin wakilcinsa al’ummar Kumbotso ke da buqata a lokacin da wakilansu ke nuna halin ko in kula, musamman idan aka yi duba da halin da jama’a ke ciki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

“Qaramar Hukumar Kumbotso tana fama da rashin wakilci nagari, kusan kowa kuka yake yi da yadda abubuwa suke tafiya. Lokacin da Umar Ballah yake wakiltarmu, ya yi muhimman abubuwa na alheri, saboda haka muka ga dacewar sake zabensa domin yana da qwarewar yin gwagwarmaya da sauran takwarorinsa ‘yan majalisu wajen ganin ya kawo wa Kumbotso cigaba.” In ji Hon Girma.

Har ila yau ya ce, tuni shiri ya yi nisa don ganin an wayar da kan al’umma a mazabu 10 da suke qaramar hukumar Kumbotso domin su sake zaben Hon Ballah.

“Yanzu idan ka duba mazabata ta Guringawa, al’umma tuni sun amsa kira, shi ya sa muke ta kokarin ganin kiranmu ya shiga lungu da saqo, kasancewar qaramar hukumarmu na buqatar a kawo mata dauki.” In ji shi.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: