-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

2019: Takarar Gwamnan Kano Abba K. Yusuf Na Cikin Tsaka Mai Wuya


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

2019 : Takarar Gwamnan Kano ta Abba K. Yusuf na cikin tsaka mai wuya

Rahoton Daily Nigerian Hausa

Dan takarar Gwamnan Kano karkashin jam’iyyar PDP Abba K. Yusuf ya auka cikin rudani, abinda ya sanya ya dauko hayar kwararren lauya mai mukamin SAN dan kare takararsa.

A ranar biyu ya watan Oktoba ne a wani yanayi mai cike da ayar tambaya, aka yi wani abu da aka kira zaben fidda gwani na dan takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP a Gidan Kwankwaso dake kan titin Lugard, kuma aka bayyana Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Sai dai kuma, mutumin da aka bayyana cewar ya zo na biyu a wannan zaben, Jafar Sani Bello ya shigar da kara gaban mai Shariah AT Badamasi yana rokon da kotun ta ayyana shi a matsayin dan takarar PDP sakamakon rashin cika ka’idar da Abba K. Yusuf yayi na shigowa PDP din.

A cewar Lauyan Jafar Sani Bello, ya bayyanawa kotu cewar Abba Kabiru Yusuf ya karya sashi na 8, karamin kashi na 8 da ya bayyana cewar tilas wanda duk ya yiwa jam’iyyar kome sai ya rubuta wasika zuwa ga Shugabancin mazabarsa domin shaida musu komawarsa jam’iyyar, abinda yace Abban bai yi ba.

A saboda haka ya roki kotun da ta ayyana Jafar Sani Bello a matsayin dan takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP sakamakon rashin bin doka da Abban yayi na komawa jam’iyyar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: