2019: Ba za ayi adalci ba muddin Buhari bai amince da gyaran dokar zabe ba – SDP

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sakataren jam’iyyar SDP na kasa Shehu Gabam, kuma abokin dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar ya ce bai tsamanin za a iya gudanar da sahihin zabe a 2019 ba saboda rashin amincewa da kudirin yiwa dokar zabe garambawul da shugaba Buhari ya yi.

Ya ce ‘yan siyasa sun dauke zabe abin Ko a mutu ko ayi rai a madadin yiwa kasa hidima ,kuma hukumar INEC da hukumomin tsaro suma duk suna taka rawa wajen tabarbarewar lamuran kuma za a iya kawo gyaran ne bayan amincewa da kudirin yiwa dokar zaben garambawul kamar yadda Tribune ta rawaito

Talla

A hirar da ya yi da Ishola Michael, Gabam ya ce,”Babu yadda za a iya gudanar da sahihin zabe idan ‘yan siyasa sun mayar da zabe abin a mutu ko ayi rai a madadin hanyar yiwa kasa hidima.

Galibin ‘yan siyasa sukan kawo cikas domin su samu nasara a zabe.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 690

“Ba INEC ce kadai matsalar ba, yan siyasa suna daga cikin wadanda ke janyo matsaloli a harkokin zabe amma shugaban kasa yaki amincewa da kudirin yiwa dokar zabe garambawul, wannan zai bawa ‘yan siyasa damar suyi dukkan abubuwan da suka ga dama.

“Duk dan siyasan da zai iya tattaro ‘yan daba shine zai tafiyar da abubuwan da za su farua rumfar zabe kamar dangwale ba bisa ka’idaba da sace akwatin zabe, abubuwan suna da yawa.

Daga lokacin da muka sanya kasa a gaba, za mu fara kirkiro dokokin da za su dabbaka demokradiyya da dawo da doka da oda da kuma adalci.”

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: