-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

2019: An Kai Ni Kotu Ne Don A Lalata Mini Siyasa – Zaura


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar GPN a jihar Kano, Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura, ya bayyana cewa, an gurfanar da shi a gaban kotu ne, ba don komai ba sai don a lalata siyasarsa, saboda yadda a ka ga ya na samun tagomashi a jihar.

A.A Zaura ya bayyana hakan ne a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano lokacin da a ka ya ke fuskantar tuhuma tare da mutane kan wasu zarge-zarge guda tara masu alaka da hadin baki da shirga karya, don amsar kudin da ya kai Dala miliyan 1.320 daga wani dan kasar waje, zargin da dan takarar ya karyata.

Bisa haka sai Zaura ya fito karara ya shaidawa kotun cewa, shi fa bai karbi kudi daga hannun kowa ba. Don haka sai ya bayyana wa kotun cewa, yakamata EFCC ko wani mutum su daina shafa ma sa kajin kaji.

A yayin da manema labarai su ka tuntube shi bayan da kotu ta bayar da beinsa, sai Zaura ya ce, “tun daga farkon batun a lokacin da a ka kai korafi na, na riga na shaida wa EFCC cewa, ban aikata laifin komai ba, kuma na jadda a gaban kotu ma cewa, dukkan laifukan da a ke zargi na da su ban aikata su ba, amma a yanzu ba zan ce komai ba tunda maganar ta na gaban kotu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

- Advertisement -

” Amma wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, batun ba zai rasa nasaba da siyasa ba, don kawai a durkusar da tasirin dan takarar jam’iyyar ta GNP a jihar, saboda ba a so ya kai labari a zaben 2019 da ke tafe. “Mu na kallon lamarin a matsayin wata dabara ta murdaddiyar siyasa, amma mu na da karfin gwiwar cewa Alhaji Zaura zai yi nasara a kotun da ma zabe mai zuwa,” in ji majiyar.

Yanzu haka dai an dage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga Janairu, 2019, don cigaba da sauraron ta.

#Leadershipayau

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: