Labarai

Babban Limamin Katolika yayi Murabus Tare da Ficewa Daga Cocin

Babban Limamin Katolika yayi murabus tare da ficewa daga cocin bayan yace ya gano ba darikar gaskiya bace.

yace gwara yabi Allah kadai domin yanason idan ya mutu ya shiga Aljannah

DAGA HAUSA TIMES: Babban Limamin Cocin Katolika reshen Uyo jihar Akwa Ibom, Patrick Edet, ya girgiza masu sauraren wa’azinshinsa na kirista da ya saba gabatarwa a tashar rediyo bayan da yace ya fice daga darikar Katolika domin ya gano ba hanyar bi bace.

 

A wa’azinsa na ranar Laraba a tashar Planet 101.1FM, Uyo, Faston ya cigaba da cewa gaskiya ta bayyanar masa cewa Allah ya wuce misali ya wuce tunanin dan Adam kuma saboda haka ya yanke shawarar Allah kadai zai bautamawa ba tare da bin dokokin coci ba.

Premium Times ta wallafa a shafinta cewa babban limamin cocin nada dumbin mabiya kuma ya share fiye da shekara 11 yana koyaswa.

Yace a mutane ne basu gane ba amma a gaskiya darikar katolika tana gindaya wasu sharudda wadanda a iyakacinsu kadai zaka tsaya wajen sanin Allah ana boye hakikanin hanyoyin sanin Allah wanda shi kuma yaga ba zai cigaba da bin wannan sharadi ba.

Zai cigaba da binciken sanin Allah tare da bauta masa ba tare da shakkar dokar coci ko kaidin wani mutum dan Adam ba.

Hausa times ta ruwaito lamarin ya tashi hankulan dumbin kiristoci mabiya darikar Katolika wacce tafi yawan mabiya a jihar Akwa-Ibom.

Edet ya cigaba da fallasa cewa ya kwashe wata da watanni yana azumi na neman zabin Ubangiji kafin daukar matakin yin murabus da ficewa daga darikar mai cike da sarkakiya da boye-boye. Yace a karshe Ubangiji ya yi masa zabi na Alheri.

A cewarsa ya shiryawa duk wata kyara da zagi da kuntatawa da zai fuskanta game da daukar matakin nashi amma tsoron Allah yafi masa duk wannan kaidin da zai fuskanta. Ya zabi yabi Ubangiji ya bauta masa domin idan ya mutu ya shiga Aljannah.