Labarai

Ɗan TikTok ya mutu bayan ya ɗaɗɗaki giya kwalaba 7 ba tare da ya tsaya ba

Ɗan TikTok ya mutu bayan ya ɗaɗɗaki giya kwalaba 7 ba tare da ya tsaya ba

 

Wani ma’abocin dandalin sada zumunta na Douyin – makwafin shafin TikTok a China – ya mutu bayan ya ɗauki kansa a bidiyo yana shan barasa kai-tsaye.

 

BBC Hausa ta rawaito cewa mutumin mai suna Brother Three Thousand ya sha kwalaba bakwai ta baiju kai-tsaye a bidiyon ranar Talata da ta wuce.

 

An tsinci gawarsa bayan awa 12 da yaɗa bidiyon nasa, a cewar wata kafar labarai a China.

 

Mutuwar tasa ta janyo ƙarin kiraye-kirayen tsaurara dokokin yaɗa bidiyo kai-tsaye a China, wurin da irin wannan ɗabi’ar ke ƙara yawaita.

 

Mutumin mai shekara 34 ya ƙware wajen shan giyar China mai suna baiju kai-tsaye a bidiyo. Baiju na ɗuke da kashi 60 cikin 100 na sinadarin alcohol.

 

A ranar 16 ga watan Mayu, ya shiga gasar shaye-shaye har huɗu, inda ma’abota shafukan sada zumunta ke fafatawa da junansu don samun kyautuka mafiya yawa daga wajen magoya bayansu a ƙanƙanin lokaci.

 

Bayan ya yi rashin nasara ne a gasar sai ya sha kwalaben baiju a matsayin horo. ‘Yan kallo sun ce ya sha kwalabe aƙalla bakwai a daren.