Labarai

Ƴan sanda sun tabbatar da rasuwar ɗan Davido

Rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce ta gayyaci mutane takwas masu hidima a gidan shahararren mawaƙin nan Davido, bisa ga rasuwar ɗan mawaƙin, mai shekara uku.

 

Mai magana da yawun rundunar Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa BBC cewar yanzu haka an ajiye gawar yaron a ɗakin ajiye gawa.

 

Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, kuma ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda.

 

Kakakin ƴan sandan ya kuma ce sun tattauna da iyayen yaron, yayin da suke ci gaba da bincike.

About the author

Sulfidone

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement