Labarai

Ƴan Sanda A Katsina Sun Kama Ƴar Jarida Bisa Zargin Ci Masu Zarafi A Shafin Tiktok

Ƴan Sanda A Katsina Sun Kama Ƴar Jarida Bisa Zargin Ci Masu Zarafi A Shafin Tiktok

 

Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina ta cika hannu da wata ƴar jarida mai suna Ruƙayya Aliyu Jibia, bisa zargin ci masu zarafi bayan ta wallafa wani faifan bidiyo a shafinta na manhajar Tiktok.

 

“A ƙwanakin baya dai idan baku manta ba, rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta kama wasu mata da ake zargi da harkar karuwanci tare da gabatar da su ga manema labarai a harabar hediƙwatar ƴan sandan jihar Katsina.

 

A sabili da haka ne Ruƙayya ta yi wani rubutu a shafin ta na Tiktok inda ta ƙalubalanci abinda ƴan sandan suka yi a matsayin cin zarafinsu da kuma take haƙƙin dan Adam.

 

Katsina Reporters ta samu rahoton cewa Ruƙayya dai ma’aikaciyace a gidan jaridar Tambarin Hausa, inda rundunar yan sandan jihar Katsina, take ci gaba da tsare ta a halin yanzu.