Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kone Gari Kurmus A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Ƴan bindiga dauke da makamai, sun kai hari a garin Yantuwaru dake gundumar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka kone gidajen garin da yammacin jiya Juma’a.

Wani mazaunin garin Rabe Ahmed Ƴantuwaru ya shaidawa RARIYA ta waya cewa yan bindiga sun kai harin da yammacin yau.

Ahmed Rabe ya ce yan bindiga sun kaddamar da harin da marecen yau, bayan yan garin sun dawo daukar sauran kayayyakinsu, daman sun kore su daga Garin, inda suke zaune garin na su da dadewa, watau mun bar garin, da suka ji mun zo daukar kayan suka kawo hari inda suka kone gidajenmu baki daya.

Rabe Ahmed Ƴantuwaru ya cigaba da cewa yanzu haka Mutum guda ya bace da shi da iyalansa matansa ukku da yara. Yan bindiga nan suka gudanar da bukukuwan Sallah a garin na mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: