Daga El farouq jakada
Wasu fusatattun ƴan bindiga sun kai mummunan hari a wata kasuwa dake garin Ƴar tasha dake gundumar Dan Sadau a Karamar hukumar Maru, inda mutum daya ya rasa ransa tareda jigata wasu da dama gamida ƙone shashen da ake sayar da dabbobi na kasuwar.
Wani mazaunin kauyen mai suna Alhaji Umaru yar tasha ya shaidawa wakilin Daily trust ƴan bindigar sun shigo kasuwar wajen karfe 2pm inda suka fara bude wa jama’a wuta.
Wannan hari yaja ƴan kasuwa da dama sunyi hasarorin dukiya marar adadi da bazata iya misaltuwa ba.