Shahararren mai rajin kare hakkin Ɗan Adam Muhammad Lawal Gusau, ya janye ƙarar da ya shigar a kan fitacciyar jaruma Rahama Sadau, bayan ta fitar da wani hoto da ya janyo batanci ga Annabi (S.A.W) a shafin ta na yanar gizo.
Muhammad Lawal Gusau, ya bayyana janye karar ne a cikin wata takarda da ya aike wa shugaban rundunar ƴan sandan Najeriya, da kwamishinan ƴan sanda na Jihar Kaduna, inda ya ce hakan ya biyo bayan matsayar da manyan Malamai su ka ɗauka ne dangane da lamarin.
Haka kuma, Lawal Gusau ya aika takardar zuwa ga wasu manyan Malamai, waɗanda su ka haɗa da Limamin masallacin Sultan Bello Sheikh Khalid Sulaiman, da na masallacin Al-Mannar Sheikh Muhammad Tukur Adam Abdullahi, da na masallacin Dahiru Bauchi Sheikh Abdulkadir Hashim Bindawa da kuma Sheikh Halliru Maraya.
Muhammad Lawal Gusau, ya ce ya janye ƙarar ne, sakamom fahimtar da aka samu, da kuma nadamar da jarumar ta yi, inda ta sha alwashin cewa haka ba za ta ƙara faruwa ba da izinin Allah.
Malaman addini dai sun bayyana mahimmancin ba Rahama Sadau uziri, musamman ganin yadda ta nuna damuwa da kuma nadamar abin da ta aikata.
-Idon Mikiya