Ƙarar Da Muka Kai Rahama Sadau Bata Da Alaƙa Da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ƙarar Da Muka Kai Rahama Sadau Bata Da Alaƙa Da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Sai Dai Ƙur’ani Da Hadisin Manzon Allah (SAW), Inji Ƙungiyar Lauyoyin Da sukayi Ƙara

Ga dukkan alamu tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau zata bayyana a gaban kotun shari’ar Musulunci dake Kaduna bisa zargin batanci ga Annabi (SAW).

A baya rahotanni sun bayyana cewa ƴan sanda na kan binciken Rahama saboda saka wasu hotuna da suka jawo aka yi ɓatanci ga Annabi (SAW).

A wata sanarwa da aka fitar wadda ta samu sa hannun Lawal Muhammad Gusau, shugaban wata ƙungiya masu ikirarin kishin addinin Islama suka fitar, sun bayyana wasu sharuɗa da Rahama zata cika kamin ta kare kanta.

Majiyar mu ta Idon Mikiya ta samu Sanarwar ta bayyana cewa kararta da aka kai bashi da alaƙa da kundin tsarin mulkin Najeriya, saidai Kur’ani da hadisin Manzon Allah (SAW).

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 405

Dole ne Lauyanta ya zama Musulmi: Dalili kuwa ƙararta da aka yi ba akan kundin tsarin mulkin Najeriya bane, akan shari’ar Musulunci da ta haɗa da Hadisin Manzon Allah (SAW) ne da kuma Qur’ani.

Ya kamata ƴan sanda su kaita kotun bayan sun kammala bincike akan lamarin.

Sheikh Nura Khalil (Digital), Dr. Ahmad Gumi, Sheikh Dr. Ahmad BUK, Dr. Isa Ali Pantami da Sheikh Kabir Haruna Gombe ne zasu bada fatawa akan batancin da akawa Annabi (SAW).

Ƙungiyar tace tana yabawa ƙungiyar Lauyoyin Arewa da basu yi katsalandan a shari’ar Aminu Sharif da Umar Farouk ba. Dan haka suna fatan wannan shari’a ta Rahama Sadau ma ba zasu shiga ba.

Sun bayyana cewa a kwantar da hankula inda suka bada tabbacin cewa shari’a zata yi aikinta.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.