Ƙananan Hukumomi 17 Daga Jihohin Katsina Da Jigawa, Sun Nemi Kafa Sabuwar Jihar Bayajidda

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Zaharaddeen Gandu
Dattawan Masarautar Daura da ke jihar Katsina, da na Masauratar Kazaure da ke jihar Jigawa sun haɗa kai, inda suke neman kafa sabuwar jihar ‘Bayajidda’.

Sun gabatar da wannan ƙudirin ne a zaman kwamitin haɗin gwuiwa da majalissun tarayya suka kafa, domin jin ra’ayoyin jama’a kan batun gyaran kunɗin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, da akayi a Kaduna.

Honarabul Lawal Ado Daura, shi ne wanda ya gabatar da ƙudirin, kuma ya shaidawa majiyar Gidauniya Tv cewa “ƙananan Hukumomi 17 ne daga Katsina da Jigawa, suke neman kafa wannan jiha”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 773

“Ƙananan hukumomin su ne guda 12 kamar haka; daga Gabas ta Arewacin Katsina, akwa Daura, Sandamu, Mai adua, Zango Baure, Kankia, Ingawa, Kusada, Mani, Bindawa, Mashi, da Dutsi. Sai kuma Ƙananan Hukumomi biyar daga Jigawa, su ne’. Kazaure, Roni, Gwuiwa, ‘Yankwashi, da Babura”.

Honarabul Lawal Ado Daura ya kuma bayyana cewa “jihar ta ‘Bayajidda’ da suke nema tana da yawan mutane sama da mutum miliyan 4”.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: